AFCON : Masar Da Afrika Ta Kudu Na Zawarcin Gasar 2019
Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta ce kasashen Masar da Afrika ta Kudu ne suka bayyana aniyarsu a hukumance ta neman karbar bakuncin gasar cin kofin AFrika na nahiyar na 2019, bayan kwace ragamar shirya gasar badi ga kasar Kamaru.
Sanarwar da hukumar ta CAF ta sanar ta ce har zuwa ranar Juma'a da karfe 12 na dare lokacin karshen wa'adin da aka bayar kasashen biyu ne kawai suka bayyana anniyarsu ta neman karbar bakuncin gasar.
Afrika ta Kudu, wacce ita kadai ce kawo yanzu wata kasa a AFrika data taba karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2010, dama ta taba karbar bakuncin gasar ta Afrika a shekarun 1996 da 2013, lokacin da ta maye gurbin Libiya wacce take fuskantar matsaloli na tsaro.
Ita kuwa Masar ta taba karbar bakuncin gasar a shekara 2006.
Sai a ranar 9 ga watan Janairu na shekara 2019 mai shirin kamawa ne, hukumar ta CAF zata sanar da kasar da zata karbi bakuncin gasar ta badi, idan Allah ya kai.
A ranar 30 ga watan Nowamba da ya gabata ne hukumar ta CAF, ta sanar da kwace ragamar gudanar da gasar ta 2019 ga kasar Kamaru, saboda tsaikon data ce ana fuskanta wajen aiwatar da wasu manyan ayyukan da kuma zaman dar dar da ake ciki a wasu yankunan kasar saboda matsalar tsaro.