Amurka Ta Bukaci Wasu 'Yan Kasarta Su Fice Daga DR Congo
Amurka ta bukaci 'yan kasarta wadanda aikinsu bai zama wajibi ba da kuma iyalensu dau fice daga Jamhuriya Demokuradiyyar Congo.
A ranar 23 ne ga watan ne kasar Congo za'a gudanar da manyan zabuka a kasar ta DR Congo, saidai ana da fargabar akan yadda zaben zai gudana, sakamakon rikice rikice da ake fama dasu a kasar.
A wata wasika data aike wa 'yan kasarta, AMurka ta ce ba tada halin tabbatar da tsaro a wasu yankuna dake wajen Kinshasa babban birnin kasar ta DR Congo, da suka hada da yankunan gabashi da kuma tsakiyar Kasai.
Dama dai yau a watan da ya gabata Amurka ta rufe ofishin jakdancinta har na tsawan mako guda saboda bazaranar ayyukan ta'addanci.
A wani labari kuma kasar Biritaniya ita ma ta shawarci 'yan kasarta dasu guji zuwa kasar ta DR Congo.