Ma'aikata A Majalisar Dokokin Najeriya Sun Fara Yajin Aiki Na Gargadi
Ma'aikata a majalisar dokokin tarayyar Majeriya sun fara yajin aiki na gargadi kuma na tsawon kwanaki hudu
Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa a yau litinin ce ma'aikatan suka fara yajin aikin, inda suka dakatar da ayyukan da suka saba gudanarwa a cikin majalisar wadanda suka hada da bangaren wuta da ruwa da kuma tsabtar majalisar.
Premium times ta ce ta ga wasu ma'aikatan suna maida wasu yan uwansu da suka shigo majalisar, amma basa tursasawa, sannan da dama wadanda suka shiga majalisar suna fitiwa bayan yan wasu mintoci.
A ranar Larabawa mai zuwa ne ake saran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatarwa majalisun dokokin kasar biyu kasasafin kudi na shekara mai zuwa. Ma'aikatan sun zabi wannan lokaci ne don samun biyan bukatunsu.
Shugaban ma'aikatan Majalisar Mr Mohammed ya ce yajin aikin zai ci gaba har zuwa ranar 20 ga watan Decemba.