Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Shari'ar William Ruto
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3448-kotun_icc_ta_yi_watsi_da_shari'ar_william_ruto
Kotun dake hukunta mayan laifuka ta duniya ta yi watsi da shari'ar da take yiwa mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto dangane da tuhumar laifukan yaki da ake yi masa.
(last modified 2018-08-22T06:58:05+00:00 )
Apr 05, 2016 11:55 UTC
  • William Ruto a kotun ICC
    William Ruto a kotun ICC

Kotun dake hukunta mayan laifuka ta duniya ta yi watsi da shari'ar da take yiwa mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto dangane da tuhumar laifukan yaki da ake yi masa.

Lauyoyin kotun ta ICC / CPI sun yi watsi da shari'ar ne kasancewar mai gabatar da kara ta kotun, Fatou Bensouda bata gabatar da isasun shaidu ba, domin ci gaba da shari'a.

Hakan ne yasa mafi yawan alkalan suka amunce da yin watsi da shari'a, aman a cewar kotun ana iya daukaka kara kan wannan matakin nan gaba gaban kotun ko kuma gaban wata kotun kasa.

Ana dai tuhumar Ruto tare da wani dan jaridan kasar, Joshua Sang da zargin hannu a kisan mutane sama da 1,300 a rikicin bayan zaben da aka fafata tsakanin shugaba Mwai Kibakida Raila Odinga a watan Desamba 2007.

Kotun dai ta yi watsi da irin wannan tuhumar da aka yi wa shugaban kasar ta Kenya, Uhuru Kenyatta, a 2014.