Ana Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu A Madagaska
A Madagaska, yau Laraba ne al'ummar kasar ke kada kuri'a a zaben shugaban kasar zagaye na biyu, inda 'yan takara tsaffin shuwagabannin kasar, Marc Ravalomanana da Andry Rajoelina ke fafatawa.
Sama da 'yan kasar miliyan goma ne suka cancanci kada kuri'a a zaben na yau.
'yan takara biyu dai sun kasance kud-da-kud a zabe zagaye na farko da aka gudanar a ranar 7 ga watan Nowamba, inda Andry Rajoelina mai shekaru 44 ya samu sama da kashi 39% na yawan kuri'un da aka kada, a yayin da Marc Ravalomanana mai shekaru 69 ya samu kashi 35%.
A ranar Litini data gabata ce aka kawo karshen yakin neman zaben, inda 'yan takara suka kwashe makwanni suna hadin kan al'umma akan su fito kada kuri'a a zaben zagaye na biyu, kasancewar ba'a samu fitowar jama'a sosai ba a zagayen farko.
Bayanai sun nuna cewa an kawo yakin neman zaben cikin kwanciyar hankali, duk da cewa wasu 'yan kasar sun nuna rashin jin dadi akan yadda 'yan takaran sukayi ta firtawa junansu kalamai marasa dadi.