DRC : Kwamitin Tsaro Ya Damu Kan Rikice-rikicen Gabanin Zabe
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna damuwa akan rikice-rikicen dake faruwa a baya bayan nan gabanin zaben shugaban kasa a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo.
A yayin da ya rage kwanaki kadan a je zaben, kwamitin tsaron na MDD, ya bukaci bangarori da batun ya shafa dasu kai zuciya nesa su daina takalar juna.
Duk da cewa kasashe mambobin kwamitin sun gamsu da ci gaba da aka samu wajen shirye-shiryen zaben, amma tare da nuna damuwa akan al'amuran dake faruwa a baya bayan nan.
Kwamitin tsaron na MDD, na dai fatan zaben na DRC na ranar 23 ga watan Disanban nan, ya kasance abin tarihi, inda wani shugaba zai mika mulki cikin ruwan sanyi ga wanda aka zaba.
A don haka kwamitin ya bukaci a baiwa ko wanne bangare damar tofa albarkacin baki da gudanar da taruka ko gangami domin kaucewa duk wani abu da zai janyo fitina.