Wani Bom Ya Fashe A Yammacin Kasar Habasha A Yau Laraba
Mutane goma ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan da motarsu ta taka nakiya a kan tati a wani yankin da aka dade ana fama da tashe-tashen hankula a kasar Habasha.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa tashin bom din ya auku ne a kan babban tati da yake kan iyakar lardunan Oromia da kuma Gumuz daga yammacin kasar.
Labarin ya kara da cewa mutum guda ya ji rauni a wannan hatsarin.
Ton shekara ta 2015 ne aka fara tashe-tashen hankula a wadannan yankuna saboda kwace filayen da aka yiwa wasu daga cikin mutanen yankin.
Ya zuwa yanzu daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu sanadiyyar matsalolin tsaro a yammacin kasar na Habasha., sannan wasu kimani dubu 100 sun kauracewa gidajensu.