Mutane 5 Sun Rasa Rayukansu A Wani Bam A Burkina Faso
Akalla mutane biyar ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai a gabashin kasar Burkina Faso.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron kasar Burkina Faso suna sanar a jiya cewa, wani bam da ya tashia jiya Asabar a garin Boungou da ke gabashin kasar, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5, da suka hada da jami'an 'yan sanda hudu da kuma farar hula guda.
An kwashe kimanin shekaru uku ana fama da hare-haren 'yan bindiga a yankunan arewacin kasar Burkina Faso, wanda daga bisani kuma lamarin ya kai zuwa gabashin kasar.
A cikin watan Agustan da ya gabata ma an kai wani harin makamancin wannan a yankin na Boungou, wanda shi ma ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an 'yan sanda 5.