An Fitar Da Sammacin Kamo Matar Tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34490-an_fitar_da_sammacin_kamo_matar_tsohon_shugaban_kasar_zimbabwe_robert_mugabe
Majiyar shari'a a kasar Afirka Ta Kudu ce ta sanar da fitar da sammacin a jiya Laraba
(last modified 2018-12-20T06:56:43+00:00 )
Dec 20, 2018 06:56 UTC
  • An Fitar Da Sammacin Kamo Matar Tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe

Majiyar shari'a a kasar Afirka Ta Kudu ce ta sanar da fitar da sammacin a jiya Laraba

Babban mai shigar da kara a kasar ta Afirka ta Kudu, ce an fitar da sammacin kamo Grace Mugabe ne saboda cin zarafi da dukan da ta yi wa wani mutumin kasar a shekarar 2017

A cikin watan Janairu na 2018 ne dai kariyar diplomasiyyar da Grace Mugabe take da ita ta zo karshe, abin da ya sa aka fitar da sammacin a wannan lokacin

Robert Mugabe ya shugabancin kasar ta Zimbabwe tun daga 1980, har tsawon shekaru 37. A ranar 21 ga watan Nuwamba ne dai sojojin kasar su ka kawo karshen mulkin Mugabe ta cikin ruwan sanyi.