Togo : 'Yan Adawa Sun Kauracewa Zaben 'Yan Majalisar Dokoki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34495-togo_'yan_adawa_sun_kauracewa_zaben_'yan_majalisar_dokoki
A kasar Togo sama da 'yan kasar miliyan uku ne da suka cancanci kada kuri'a ke zaben 'yan majalisar dokoki a yau Alhamis.
(last modified 2018-12-20T07:46:52+00:00 )
Dec 20, 2018 06:45 UTC
  • Togo : 'Yan Adawa Sun Kauracewa Zaben 'Yan Majalisar Dokoki

A kasar Togo sama da 'yan kasar miliyan uku ne da suka cancanci kada kuri'a ke zaben 'yan majalisar dokoki a yau Alhamis.

'Yan kasar na kada kuri'a ne domin zabar wakilansu a majalisar dokokin kasar data kunshi kujeru 91.

Bayanai daga kasar sun ce an tsaurara kwararen matakai na tsaro inda jami'an tsaro ciki har da na soji ke sintiri a manyan biraren kasar.

Saidai bayanai sun ce zaben baida wani armashi, kasancewar kawancen jam'iyyun adawa na kasar su 14, sun kaurace wa zaben.

'Yan adawan dai na da korafi ne akan dokar wa'adin mulki na shugaban kasa, wacce take baiwa shugaban kasar Faure Gnassingbe sake tsayawa takara don neman wani wa'adin mulki.