An Kashe Mutum Guda A Harin Yan Bindiga A Jihar Zamfara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34499-an_kashe_mutum_guda_a_harin_yan_bindiga_a_jihar_zamfara
Yan bindiga sun kai hare-hare kan wurare ukku a karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara na tarayyar Najeriya a jiya Laraba inda suka kashe mutane da dama wadanda suke aiki a gonan dankalin turawa.
(last modified 2018-12-20T19:03:05+00:00 )
Dec 20, 2018 19:03 UTC
  • An Kashe Mutum Guda A Harin Yan Bindiga A Jihar Zamfara

Yan bindiga sun kai hare-hare kan wurare ukku a karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara na tarayyar Najeriya a jiya Laraba inda suka kashe mutane da dama wadanda suke aiki a gonan dankalin turawa.

Jaridar Premuim times ta Najeriya ta nakalto wata majiya tana fadar haka a yau Alhamis ta kuma kara da cewa a Garin Haladu yan bindigan sun zo da misalin karfe daya na rana, sannan suka bude wuta kan manoma inda a nan take suka kashe mutane 10.

Labarin ya kara da cewa da yamma kuma yan bindigan sun sake dawowa inda suka rufe Garin Kaka da kuma Nasarawa Godal, insa suka kashe mutane 13 a garuruwan biyu. 

Wani wanda bai sun a bayyana sunansa ya fadawa Premium times cewa wadanda yan bindigan suka kashe a Nasarawa Godal su hudu ne, kuma su ne Kurma Garba, Sunusi Mairoba, Ibrahim Yahuza kuma Haruna Dangodal.

Laraban ya kammala da cewa wadanda rauninsu yake da tsanani an kaisu babban asbitin Kauran Namoda.