An Dage Zaben Shugaban Kasa A D.R Congo
Hukumar zabe mai zaman kanta a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, cewa da (CENI), ta sanar a hukumance da dage zaben shugaban kasar har zuwa ranar 30 ga watan Disamban nan da muke ciki.
Tunda farko dai an shirya za'a gudanar da zaben ne a ranar 23 ga watan na Disamba, saidai a taron manema labarai data kira, hukumar ta CENI, ta ce lokaci ba zai ishe ta ba ta gudanar da zaben kamar yadda aka tsara tunda farko saboda matsalar kayan aiki.
Shugaban hukumar ta CENI, Corneille Nangaa, ya bayyana cewa, gobara da aka samu kwanan baya a cibiyar adana kayan zabe a Kinshasa ta haddasa barna ta kuri'u masu yawa, inda yanzu haka an yi odar takardun zabe, kuma ye zuwa ranar 19 ga watan nan an samu miliyan guda, sannan sauren ba zasu iya samu ba sai ranar 22 ga watan Disamba da yamma.
Kuma a cewarsa akalla sai cikin sa'o'i 60 za'a iya rabasu, a don haka ne fatanmu a gudanar da zaben a ranar 30 ga watan na Disamba.
Tuni dai wasu jam'iyyun adawa na kasar suka bayyana rashin amincewarsu da duk wani yunkuri na jinkirta zaben.