Sudan : An Kafa Dokar Hana Fitar Dare bayan Zanga-zangar Tsadar Rayuwa
Hukumomi a Sudan sun sanar da ayyana dokar hana fitar dare a yankin Atbra bayan mummunar zanga zangar kan tsadar rayuwa data barke a wasu biraren kasar.
Dokar dai ta tanadi hana fitar dare daga karfe 6:00 na yamma har zuwa 6:00 na safe
Rahotanni daga kasar sun ce akalla mutum shida ne suka mutu a yayin zanga zangar da aka fara a ranar Laraba.
Masu zanga zangar dai na nuna bacin ransu kan tsadar rayuwa, data shafi karin kudi kan farashin biredi.
Bayanai daga kasar sun ce masu zanga zangar sun sanya wuta kan cibiyar jam'iyya mai mulki a birnin na Atbra.
Masu zanga zangar da suka hada da dalibai sun kona tayoyi akan tituna tare da firta kalaman nuna adawa da tsadar rayuwa.
"yan sanda sunyi amfani da kulakai domin tarwatsa masu zanga zangar.