Gabon : Guy Nzouba Zai Tsaya Takara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3451-gabon_guy_nzouba_zai_tsaya_takara
kwanaki kadan da yin murabus daga matsayinsa na kakakin majalisar dokokin kasar Gabon Guy Nzouba Ndama ya bayana aniyar sa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasa dake tafe.
(last modified 2018-08-22T06:58:05+00:00 )
Apr 05, 2016 12:43 UTC
  • tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Gabon Guy Nzouba
    tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Gabon Guy Nzouba

kwanaki kadan da yin murabus daga matsayinsa na kakakin majalisar dokokin kasar Gabon Guy Nzouba Ndama ya bayana aniyar sa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasa dake tafe.

Mr Nzouba wanda sanannan dan siyasa ne daya shafe shekaru 20 a shugabancin majalisar dokokin wannan kasa, ya kuma sanar da janyewarsa daga jam'iyyar PDG mai mulki.

Hakan dai ya sanya tsohon kakakin majalisar dokokin kasar shiga cikin jerin wadanda zasu fafata da shugaban kasar mai barin gado Ali Bango dake neman wa'adi na biyu.

kawo yanzu dai ba'a sanar da ranar da za'a gudanar da zaben ba a hukumance, aman wasu majiyoyi kusa da gwamnatin kasar sun ce ana sa ran gudanar da zaben a cikin watan Agusta mai zuwa.

A makon daya gabata ne kakakin majalisar dokokin kasar ta Gabon Guy Nzouba Ndama ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon abin da ya kira shishshigi da bangaren zartaswa ke yi wa harkokin majalisa.