Zanga Zangar Sudan : Mutum 22 Suka Mutu, Inji Madugun 'Yan Adawa
(last modified Sat, 22 Dec 2018 14:28:01 GMT )
Dec 22, 2018 14:28 UTC
  • Zanga Zangar Sudan : Mutum 22 Suka Mutu, Inji Madugun 'Yan Adawa

Madugun 'yan adawa a Sudan, Sadek al-Mahdi, ya bayyana cewa mutum 22 ne suka mutu a zanga zangar tsadar rayuwa data barke a baya bayan nan a wasu biranen kasar.

Da yake sanar da hakan a wani taron manema labarai yau Asabar, a birnin Oumdourman, dake makobtyaka da Khartoum babban birnin kasar, madugun 'yan adawan ya ce zanga zangar ta haifar da mutuwar mutum 22 da kuma raunata wasu da dama, saidai ba tare da yin wani karin bayyani ba.

Jagoran jam'iyyar ta Al'umma, ya ce zanga zangar da ake halattaciya ce, kuma anayinta ne saboda tabarbarewar harkokin tattalin arziki da kuma na rayuwar jama'a a kasar, tare da shan alwashin cewa za'a ci gaba da zanga zangar.

Matakin gwamnatin kasar na kara kudin biredi a cikin makon nan ne dai ya janyo zanga-zanagr jama'ar kasar wacce ta fara a ranar Laraba data gabata.

Bayanai sun nuna cewa darajar kudin kasar ya fadi da kusan kashi 70% igaban dalar Amurka.