Madagaska : Rajoelina Na Daf Da Yin Nasara A Zaben Shugaban Kasa
Sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Madagaska, na nuni da cewa dan takara Andry Rajoelina, na daf da samun nasara a zaben, inda ya yi wa abokin hamayarsa Marc Ravalomana fintinkau.
Alkalumman wanda na wucin gadi ne da hukumar zaben kasar ma zamen kanta CENI ta fitar dazu da rana sun nuna cewa tsohon shugaban kasar, Andry Rajoelina na kan gaba da kashi 55%.
Saidai tuni abokin hamayarsa, Marc Ravalomanana wanda kawo yanzu yake da kashi 44,2% ya yi fatali da sakamakon zaben wanda ya ce an tafka magudi da murdiya a ciki.
Ana sa ran nan da bikin Kirsimeti dake tafe ne hukumar zaben kasar zata bayyana sakamakon dindin-din na zaben.
Tuni dai magoya da makusantan dan takaran dake gaba cewa da Andry Rajoelina suka fara murna yin nasara a zaben, kasancewar a cewarsa babu wani babban sauyi da za'a samu a sakamakon zaben na dindin-din da ake jira.