Taron Shuwagabanin Kungiyar ECOWAS Karo Na 54
Shugabannin kasashen Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, wato ECOWAS sun gudanar da wani taron yini guda a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.
Taron wanda shugaban Najeriya Buhammadu Buhari ya jagoranta yau Asabar, ya tattauna batutuwan da suka shafi yankin na yammacin Afirka.
Manyan batutuwan da taron karo na 54 ya maida hankali, sun hada da batun nan na samar da kudin bai-daya tsakanin kasashen yankin, da kuma batun rikicin siyasa a kasashen Togo da Guinea Bissau.
Kwamatin da Kungiyar ta ECOWAS ta kafa domin lalubo mata dalilin da ya sa kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar ke samun koma-baya, ya bayyana rashin samar da kudin-bai-daya a matsayin babbar matsalar da ke hana cinikayya samun nasara a yankin.
A bangare guda, shugaba Buhari mai masaukin baki ya jaddada aniyarsa ta gudanar da sahihin zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.