Sudan: Masu Zanga-zanga Sun Kwace Iko Da Gundumar Nilul-Abyadh
(last modified Sun, 23 Dec 2018 06:46:29 GMT )
Dec 23, 2018 06:46 UTC
  • Sudan: Masu Zanga-zanga Sun Kwace Iko Da Gundumar Nilul-Abyadh

Kafar watsa labaru ta Alrakoba ta ce; Zanga-zangar da ake yi ta tilastawa gwamna jahar ta White Nile da iyalansa guduwa zuwa wani wuri da ba a san ko'ina ba ne

Masu Zanga-zangar da suka iko da gundumar sun kone gidan gwamna da wasu gine-gine na gwamnatin kasar da suke a wannan jahar

Gundumar ta White Nile mai mutane miliyan biyu tana a yankin kudu masu gabashin kasar ta Sudan ne,a kudu da birnin Khartum

 Kafar watsa labarun ta Alrakoba ta ce a cikin garin al-qaradhif kadai jami'an tsaron sun kashe masu Zanga-zanga 16 da kuma jikkata wasu 30

Sai dai majiyar gwamnatin kasar ta ce wadanda su ka rasa rayukansu a sanadiyyar Zanga-zangar ba su wuce 8 ba, amma shugaban jam'iyyar adawa ta Ummah, Sadiqul Mahadi ya ce adadin mutanen ya kai 22

Tun ranar Larabar da ta gabata ne dai mutanen Sudan su ka fara gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da karin kudin biredi da kuma tsadar rayuwa

Tun dai gwamnatin kasar ta Sudan ta kafa dokar ko ta kwana a cikin wasu jahohin kasar