Burutai: Dangantaka Tsakanin Sojojin Najeriya Da Hukumar UNICEF Bata Yi Tsami Ba
Babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Tukur Brutai ya bayyana cewa dangantaka tsakanin sojojin Najeriya da kuma hukumar UNICEF ta Majalisar dinkin duniya bata yi tsami ba.
Kamfanin dillanicn labaran NAN ta gwamnatin Najeriya ta nakalto babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya yana fadar haka a birnin Maiduguri a wani taron girmama iditoci da yan jaridu na sojojin Najeriya.
Brutai yana maida martani ne kan matsalar da aka samu tsakanin sojojin Najeriya da kuma hukuma, mai kula da yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF a birnin Maiduguri a kwanakin bayan.
Burutai ya kara da cewa sojojin Najeriya a shirye suke su yi aiki da kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa, amma kuma ba zasu manta da tsaron cikin gida ba. Ya kuma kara da cewa yakamata wadannan kungiyoyi su maida hankali da ayyukansu, don kada hakan ya shafi tsaron kasarmu.
Brutai ya tabbatar da cewa sojojin Najeriya suna aiki tare da wadannan kungiyoyi don ganin sun aiwatar da ayyukansu cikin tsanaki da kuma kwanciyar hankali. Ya ce sojojin Najeriya suna rakiyar jami'an kungiyoyin bada agaji zuwa wasu wuraren da ba zasu iya zuwa ba sai da jami'an tsaro don ganin sun yiwa yara kanana alluran riga kafi ko sun kai dauki ga wasu mabuta a yankunan.
Daga karshe babban komandan ya bayyana cewa an warware matsalar da ta taso tsakanin hukumar UNICEF da sojojin Najeriya da fatan hukumar za ta yi hattara don kada a sake samun irin wannan sabanin.