Togo : Jam'iyya mai Mulki Ta Samu Rinjaye A Zaben Majalisar Dokoki
Dec 25, 2018 13:06 UTC
Hukumar zabe mai zaman kanta a Togo ta sanar da sakamakon wucin gadi na zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka kada kuri'arsa a ranar 20 ga watan Disamban nan.
Sakamakon wanda na wucin gadi ne ya ce jam'iyya mai mulki a kasar ce ta samu rinjaye inda ta samu kujeru 59 dga cikin 91 da majalisar dokokin kasar ta kunsa.
Sakamakon kuma ya kuma nuna cewa jami'iyyun 'yan ba ruwanmu da kuma na 'yan adawa sun samu kujeru 32.
Zaben wanda gungun jam'iyyun adawa suka kaurace wa ya samu fitowar jama'a da kashi 59,25%.
'Yan takara 850 ne suka fafata a zaben na 'yan majalisar dokoki.
A nan gaba ne kotun tsarin mulkin kasar zata bayyana matsayinta akan zaben.
Tags