Yan Bingida A yankin Niger Delta Sun Yi Barazanar Hargiza Zaben 2019
Mayakan wata sabuwar kungiya dauke da makamai a yankin Niger-Delta a tarayyar Najeriya ta yi barazanar rikata zaben shekara ta 2019 idan gwamnatin tarayyar bata amsa kiranta ba.
Kamfanin dillancin labaran NAN na gwamnatin Najeriya ta nakalto majiyar kungiyar "War Against Niger Delta Exploitation (WANDE) tana fadar haka a ranar talata a birnin Port Hacourt na jihar Rivers.
Kakin kungiyar Mr Nomukeme ya yi gargadin cewa kungiyarsa zata fara tashe-tashen hankula a kasar idan har gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari bata amsa kiranta na fara wani shiri na raya yankin Niger-Delta mai arzikin man fetur ba.
Mr Nomukeme , ya kara da cewa an dade ana hana mutanen yankin arzikin da Allah ba basu, amma a wannan karon mutanen yankin ba zasu ci gaba da zama bayi ga gwamnatin tarayyar kasar ba.
Daga karshe kakakin kungiyar ya kammala da cewa gwamnatin shugaba Muhammadu buhari zata ci gaba da samun goyon bayan kungiyar idan har ta cika bukatunta guda 7 da ta zayyana.