Mayakan Boko Haram Sun Kwace Wasu Wurare A Jihar Borno
Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa mayakan kungiyar Boko Haram a tarayyar Najeriya sun kwace wasu garuruwa daga cikin har da garin Baga a arewa maso gabacin jihar Borni , sun kuma kafa tungarsu a can.
Tashar talabijin ta BBC Ingilishi ta bada labarin cewa mayakan kungiyar ta Boko Haram sun mamaye wasu yankuna a jihar Borno, inda suka tarwatsa sojojin da suke da sansaninsu a cikin yankin.
Sai dai bbc hausa ya nakalto kakakin rundunar sojan kasa ta Najeriya Janar Sani Kukasheka Usman yana cewa Boko Haram ba ta kwace garin ba, amma suna ci gaba da wani aiki a garin, kuma nan gaba za su yi karin bayani kan halin da ake ciki.
A farkon makon da muke ciki ma mayakan kungiyar ta BOKO haram sun kai hare-hare masu yawa a yakin arewa maso gabacin tarayyar ta Nigeriya inda suka kashe fararen hula biyu suka kuma tilastawa mazauna wasu kauyuka a yankin barin gidajensu.