Najeriya: An Kama Wanda Ya Kashe Air Marshal Alex Badeh
Jami'an Yansanda A Najeriya sun bada sanarwan kama mutane 5 dangane da kisan Air Marshal Alex Badeh, Tsohon Babban Jami'in Tsaron kasar
Kamfanin dillancin labaran NAN na Najeriya ya nakalto majiyar yansanda na cewa an kama mutane 5 daga cikin wadanda ake tuhuma da kashe toshon babban jami'an tsaron kasar Alex Cadeh.
Daya daga cikin mutanen da aka kama mai suna Shu'aibu Rabi dan shekara 25 a duniya ya yi magana da harshen hausa yana cewa wani abokinsa Chiroma ne ya bashi labarin cewa tsohon jami'an tsaron zai zo da kudade masu yawa don sayan fili a rana 18 ga watan Decemba.
Da haka kuma suka tsareshi a kan hanya suka kuma kashe shi da bindiga sannan suka debi kudadenda ya ce bai taba ganin yawansu ba.
An kashe Air Marshal Alex Badeh dan shekara 61 a duniya a ranar 18 ga watan Decemban da muke ciki a tsakanin garuruwan Koso and Kugwaru na jihar Nasarawa.
Bayan jin labarin Kisan shugaban Muhammadu Buhari ya yi bakin ciki da hakan, sannan ya bada umurnin a kama wadanda suka yi kissan.