An Gudanar Da Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati A Kasar Senegal
Dubban mutane ne su fito kan titunan birnin Dakar suna masu yin kira da a gudanar da zaben shugaban kasa da babu magudi a ciki
Zanga-zangar ta zo ne adaidai lokacin da ake tsammanin majalisar koli ta tsarin mulkin kasar za ta soke sunayen wasu fitattun 'yan adawa biyu daga cikin wadanda za su yi goyayya da shugaba Macky Sall a zaben shugaban kasa
Masu Zanga-zangar suna son ganin an yi zaben da babu kumbiya-kumbiya ko magudi a ciki a ranar 24 ga watan Fabrairu
Bugu da kari masu Zanga-zangar sun daga kwalaye da suke dauke da taken yin tir da tsarin kama-karya, da kuma yin kira da a saki fursunonin siyasa
Fitattun 'yan hamayyar siyasar da masu fafutuka ne su ka halarci Zanga-zangar
A ranar 21 ga watan Febrairu ne ake sa ran cewa majalisar koli ta tsarin mulkin kasar Senegal za ta sanar da sunayen karshe na 'yan takarar shugaban kasa