DRC : 'Yan Adawa Sunyi Fatali Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya Kan Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34606-drc_'yan_adawa_sunyi_fatali_da_yarjejeniyar_zaman_lafiya_kan_zabe
Jiga jigan 'yan takara jam'iyyun adawa na zaben shugaban kasa a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, sunki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a yayin babban zaben kasar dama bayansa.
(last modified 2018-12-29T15:47:30+00:00 )
Dec 29, 2018 15:47 UTC
  • DRC :  'Yan Adawa Sunyi Fatali Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya Kan Zabe

Jiga jigan 'yan takara jam'iyyun adawa na zaben shugaban kasa a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, sunki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a yayin babban zaben kasar dama bayansa.

Mayan 'yan adawa da suka hada da Martin Fayulu da Felix Tshisekedi, sun ce ba'ayi aiki da bukatunsu ba a cikin yarjejeniyar data tanadi kaucewa tashin hankali a babban zaben kasar.

Bayanai sun nuna cewa tuni dan takaran jam'iyya FCC mai mulki Emmanuel Ramazani Shadary da hukumar zaben kasar suka rattaba wa yarjejeniyar hannu a yau Asabar.

Shugaban hukumar zaben kasar ta CENI, Corneille Nangaa, ya ce yarjejeniyar ta tanadi gudanar da zaben cikin haske, da kuma kaucewa tada rikici.

Mista Nangaa ya kara tabbatar cewa babban zaben kasar zai gudana a gobe lahadi 30 ga wata.

Wadanda suka halarci taron sanya hannu kan yarjejeniyar sun hada da manyan 'yan takara shugaban kasar uku, da shugaban hukumar zaben kasar, da kuma mai shiga tsakani na ungioyar ci gaban kasashen tsakiyar Afrika, saidai rahotanni sun ce an hana wakiliyar MDD a kasar ta Congo shiga zauren taron.