Shagari: Buhari Ya Bukaci A Sauke Tuta Kasa Kadan Don Rasuwar Shagari
Shugaba Muhammadu Buhari a tarayyar Najeriya ya bukaci a sauke tutar kasar kasa-kasa don girmama tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari wanda ya rasu a ranar Jumma'an da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran NAN na Najeriya ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya je birnin Sokoto a yau Lahadi inda ya isar da ta'aziyyarsa ga iyalan tsohon shugaban kasar.
Banda haka shugaban ya bukaci ofisodhin gwamnatin da jami'an tsaro kasar da su sauke tutar kasar kasa-kasa na tsawon kwanaki ukku don girmama marigayi Alhaji Shehu shagari.
A ranar asabar ne aka yi jana'izar tsohon shugaban kasar a birnin Sokoto, kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, sannan gwamnatin tarayyar ta aika da tawaga ta musamman karkashin sakataren Gwamnati Mr Boss Mustafa don halattar jana'izar.
Har'ila yau gwamnatin jihar sokoto ta bada hutu gobe litinin 31 ga watan Decemba don yi wa tsoshin shugaban kasar addu'a.