An Fara Kidayar Kuri'un Zabe A D.R Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34620-an_fara_kidayar_kuri'un_zabe_a_d.r_congo
A Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, an fara kidayar kuri'un zaben shugaban kasa gami dana 'yan majalisar dokoki da kuma na wakilan kananen hukumomi da aka kada kuri'arsa a jiya Lahadi.
(last modified 2018-12-31T06:28:18+00:00 )
Dec 31, 2018 03:43 UTC
  • An Fara Kidayar Kuri'un Zabe A D.R Congo

A Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, an fara kidayar kuri'un zaben shugaban kasa gami dana 'yan majalisar dokoki da kuma na wakilan kananen hukumomi da aka kada kuri'arsa a jiya Lahadi.

Tun dai kafin aje ko ina manyan jam'iyyun adawa sun fara kalubalantar yadda zaben na jiya ya gudana.

Rahotanni sun nuna cewa an samu rikici a wasu sassa a yayin zaben inda mutum hudu suka mutu a lardin Walungu, dake kudancin Kivu.

Ko baya ga hakan an samu matsaloli wajen gudanar da zaben wadanda suka hada da matsalar na'urar zabe da, tsaiko wajen bude runfunan zabe da kuma hana masu sanya ido shiga wjen kidayar kuri'u.

Saidai duk da hakan shugaban hukumar zaben kasar ta (CENI), Corneille Nangaa, ya yaba da yadda zaben ya gudana.

Bayanai dai sun nuna cewa an samu fitowar jama'a sosai a zaben.

Jim kadan bayan da ya kada kuri'a, dan takaran jam'iyya mai mulki Emmanuel Ramazani, ya shelanta cewa tuni ya lashe zaben.

Shi kuwa Felix Tshisekedi, daya daga cikin manyan 'yan takara adawa na kasar cewa ya yi zaben ya gudana cikin mawuyacin hali, a yayin da shi ma Martin Fayulu shi ma na wata babbar jam'iyyar adawa ke cewa sun gano runfunan zabe na bogi da dama.

A jiya ne dai al'ummar kasar ta Jamhuriya Demokuradiyyar Congo sama da Miliyan 38,5 da suka cancanci yin zabe suka kada kuri'a a babban zaben kasar domin zabar wanda zai maye gurbin shugaba Joseph Kabila, bayan shafe shekaru biyu na jiran zaben da akayi ta dagewa har sau uku.

Kafin nan da ranar 6 ga watan Janairu na shekara mai shirin kamawa ne ake sa ran hukumar zaben kasar zata fitar da sakamakon zaben.