Jan 02, 2019 09:33 UTC
  • Al'Shabab Ta Kai Wa Ofishin MDD Hari A Mogadisho

Kungiyar Al'shabab ta dauki alhakin kai wa ofishin MDD na Mogadisho harin rokoki, wanda ya hadassa jikatar mutum uku.

Rahotanni sun nuna cewa rokoki bakwai ne kungiyar ta harba kan ofishin a jiya Talata, lamarin da ya haddasa kuma barna mai yawa ga ginin mai cikaken tsaro.

Wakilin MDD, a kasar ta Somaliya, Nicholas Haysom, ya yi tir da allawadai da harin da kungiyar ta Al'shabab ta dauki alhakin kaiwa.

Sanarwar da wakilin na MDD, ya fitar, ta ce kai hari kan cibiyoyin MDD, keta dokokin kasa da kasa ne.

Kasar Somaliya dai ta jima tana fuskantar hare hare daga kungiyar ta Al'shabab dake da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Al Qaeda. 

Tags