Sojojin Najeriya: Mayakan Boko Haram Basu Fi Sojojin Najeriya Kyawun Makamai Ba
Majiyar sojojin Najeriya ta bayyana cewa sojojin kasar sun fi mayakan boko haram a dabarbaru da kuma kyauwun makamai.
Kamfanin dillancin labaran NAN na Najeriya ya nakalto kakakin sojojin Najeriya Brigadier-General Sani Kukasheka Usman yana fadar haka a wani jawabin da yayiwa yan jaridu dangane da farfagandandar da wasu kafafen sadarwa da na yada labarai suke na cewa mayakan Boko Haram sun fi sojojin Najeriya ingantattun makamai, da nufin kashe guiwarsu.
Usman ya kara da cewa sojojin Najeriya, nesa ba kusa ba sun fi mayakan boko haram samun horo da kuma makamai da dabarbarun yaki. Ya kuma karyata jita-jitan da ake yadawa na cewa Boko Haram tana da makaman da sojojin Najeriya basa da Irinsu, don haka ne kuma take samun damar kai masu hare-hare a cikin yan watannin da suka gabata.
Kakakin sojojin ya zargi wasu mutane daga ciki da kuma wajen kasar da yada wadannan labarai na kariya, watakila saboda siyasa ka wani dalilin daban don nuna cewa sojojin Najeriya sun gaza, ko gwamnatin kasar ta gaza.
Daga karshe Usman yace yada wadannan jita-jita wani nau'i ne na yaki kwakwalwa don kashe guiwar sojojin kasar, amma ko kadan wannan ba zai yi tasiri a kan sojojin kasar ba.