Zanga-zangar Adawa Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Madagaska
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34685-zanga_zangar_adawa_da_sakamakon_zaben_shugaban_kasa_a_madagaska
Rahotanni daga Madagaska na nuni da cewa rikici ya barke a wannan Asabar tsakanin magoya bayan dan takaran da ya sha kaye a zagaye na biyu na zaben shugaban, Marc Ravalomanana, da kuma jmai'an tsaro wadanda sukayi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga zangar.
(last modified 2019-01-05T12:42:18+00:00 )
Jan 05, 2019 12:42 UTC
  • Zanga-zangar Adawa Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Madagaska

Rahotanni daga Madagaska na nuni da cewa rikici ya barke a wannan Asabar tsakanin magoya bayan dan takaran da ya sha kaye a zagaye na biyu na zaben shugaban, Marc Ravalomanana, da kuma jmai'an tsaro wadanda sukayi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga zangar.

Bayanai sun nuna cewa wannan kusan shi ne karo na biyar a cikin mako guda, da daruruwan magoya bayan tsohon shugaban kasar ke bijirewa dokar hana zanga zanga a babban dandalin ranr 13 ga watan Mayu dake Antananarivo babban birnin kasar.

Masu zanga zangar na nuna adawa ne da sakamakon da hukumar zaben kasar ta sanar na zaben shugaban kasar zagaye na biyu, da aka gduanar a ranar 19 ga watan jiya, wanda ya bayyana dan takara kana Andry Rajoelina a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sakamakon zaben da hukumar ta CENI, ta fitar ya nuna cewa dan takara, Andry Rajoelina ya lashe zaben da kashi 55,66% , a yayin da babban abokin hamayarsa Marc Ravalomanana, ya samu kashi 44,34% na yawan kuri'un da aka kada.

Masu zanga zangar dake adawa da sakamakon zaben, na matsin lamba ne ga kotun tsarin mulkin kasar akan kada ta amince da sakamakon zaben wanda a cewarsu yana cike da magudi.

A ranar Talata mai zuwa ce ake sa ran kotun tsarin mulkin kasar zata bayyana matsayinta na yin na'am ko kuma watsi da sakamakon zaben.