Zaben Congo : Amurka Na Shirin Tura Sojoji
Amurka ta sanar da jibge sojoji a kasar Gabon a wani mataki da ta ce na kasancewa cikin shiri ne, ko da kuwa rikici ya barke bayan zabe a Jamhuriya Demkuradiyyar Congo.
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban kasar Donald Trump, ya aike wa shugabannin majalisar dokokin kasar, inda ya ce tuni wani gungun farko na sojojin kasar mai kunshe da dakaru 80 ya isa a kasar Gabon.
A cewar Trump an aike da sojojin ne domin kare Amurkawa da kuma jami'an diflomatsiyyan kasarsa a Kinshasa babban birnin kasar ta DR Congo.
Shugaba Trump ya kuma ce sojojin zasu ci gaba da kasancewa a yankin har sai al'amuran tsaro sun daidaita.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban kasa da aka kada kuri'arsa a ranar 30 ga watan Disamba da ya gabata.
A gobe Lahadi ne ake sa ran hukumar zaben kasar ta DR Congo zata sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar, saidai ta ce za'a iya fuskantar tsaiko wajen sanar da sakamakon saboda matsalolin da ake fuskanta wajen kidayar kuri'un.
Tuni dai bangarorin daban daban na al'umma a kasar irinsu kungiyar (Cenco), ta mabiya addinin Katolika suka bukaci hukumar ta CENI data sanar da sakamakon cikin gaskia da bin shari'a.
Kungiyar ta (Cenco), wacce ta aike da masu sanya ido a runfunan zabe a lokacin zaben, ta ce ta riga ta san wanda ya lashe zaben , saidai ba tare da bayyana sunansa ba.