Sai A Makon Gobe, Za'a Sanar Da Sakamakon Zaben Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34687-sai_a_makon_gobe_za'a_sanar_da_sakamakon_zaben_congo
Hukumar zabe mai zaman kanta ta (CENI), a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, ta sanar da dage sakamakon babban zaben kasar da mako guda.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jan 05, 2019 17:17 UTC
  • Sai A Makon Gobe, Za'a Sanar Da Sakamakon Zaben Congo

Hukumar zabe mai zaman kanta ta (CENI), a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, ta sanar da dage sakamakon babban zaben kasar da mako guda.

A gobe Lahadi ne aka shirya za'a sanar da sakamakon wucin gadi na zaben, saidai a cewar shugaban hukumar zaben kasar, Corneille Nangaa, hakan ba zai yi wu ba zuwa gobe, sai nan da mako guda.

Mista Nangaa, wanda bai bayyana takaimaimai wace rana za'a sanar da sakamakon a nan da mako gudan, ya ce ana samun ci gaba, amma ba a samu dukkan sakamakon ba, don yanzu haka ana wajen kashi 45 zuwa 48 na kidayar kuri'un.

Zaben da aka gudanar a ranar 30 ga watan Disamba da ya gabata, shi ne dai zai bayyana wanda zai gaji shugaba mai barin gado Joseph Kabila.

Manyan 'yan takaran zaben sun hada da tsaohon ministan cikin gida na kasar, Emmanuel Ramazani Shadary, dake samun goyan bayan shugaban mai barin gado Kabila, sai kuma 'yan takara adawa guda biyu da suka hda da Martin Fayulu da Felix Tshisekedi.

Kawo yanzu dai hukumar zaben kasar ta CENi, na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin cikin gida dana kasa da kasa da suka hada kungiyar tarayya Afrika da kuma takwararta ta Turai, akan ta bayyana sakamakon gaskia wanda ya tanadi zabin al'ummar kasar ta D.R Congo.