Pira Ministan Kasar Togo Ya Yi Murabus
(last modified Sun, 06 Jan 2019 07:04:23 GMT )
Jan 06, 2019 07:04 UTC
  • Pira Ministan Kasar Togo Ya Yi Murabus

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya amince da murabus din Pira minista Selom Komi Klassou

Sai dai shugaban kasar ya bukaci Pira minista Klassou da ya ci gaba da rike gwamnati har zuwa lokacin da za a nada wanda zai maye gurbinsa

Tsarin mulkin kasar ta Togo ya bai wa shugaban kasa ikon nada pira minista a duk lokacin da ya ga dama ba tare da kayyade masa lokaci ba.

Kasar Togo tana fama da rikicin siyasa tun a 2017.

A zaben da aka gudanar a karshen watan Disamba 2018 kawancen jam'iyyu 14 na adawa, ya kauracewa zaben

Jami'iyyun sun bayyana cewa ba za su yi furuci da sabuwar majalisar dokokin kasar da za a kafa ba wacce za ta fara aiki daga ranar 8 ga watan Febrairu mai zuwa.

Bugu da kari jam'iyyun siyasar sun tsayar da ranar 12 ga watan nan na January domin gudanar da gagarumar Zanga-zangar yin kira da a samar da sauye-sauye a siyasar kasar da kuma sake gudanar da zabe mai tsafta