Gamabiya Ta Yi Maraba Da Fadada Dangantaka Da Kasar Cana
Shugaban kasar Gambiya Adama Narrow ya yi maraba da karfafa dangantakar kasarsa da kasar Cana.
Tashar talabijin ta CCTV na kasar Cana ya nakalto shugaban kasar ta Zambiya yana fadar haka a ganawarsa da ministan harkokin waje na kasar Cana Wang Yi wanda ya kai ziyarar aiki a kasar ta Gambiya a jiya Asabar.
Shugaban kasar na Gambiya ya bayyana cewa a cikin watanni 9 da suka gabata ya kai ziyarar aiki har sau biyu a kasar Cana, inda ya tabbatarwa kasar matsayin kasarsa na amincea da siyasar kasar Cana na dunkulalliyar kasar ta Cana, sannan zata ci gaba da kare muradun kasar ta Cana a fagen kasa da kasa da kuma MDD.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Cana Wang Yi ya bayyana amincearsa da siyasar kasar Gambiya dangane da kasar Cana, sannan ya bayyana cewa kasarsa a shirye take kasashen biyu su amfani juna a bangarori daban- daban.