An Shiga Sabuwar Marhala A Rikicin Kasar Sudan.
A dai-dai lokacinda mutanen kasar sudan suke ci gaba da zanga-zangar neman shugaban kasar Umar Hassan El-Bashir ya sauka daga mukaminsa, shugaban ya fara sauye-sauyen a cikin jami'an gwamnatin kasar.
Majiyar muryar JMI ta bayyana cewa shugaba Umar El-Bashir, a jiya Asabar ya sauke Mohammad Abu Zaid Mustafa ministan kiwon lafiya saboda abinda ya kira tsadar magunguna a kasar.
Banda haka shugaban ya gabatar da sauye-sauye a cikin shuwagabannin ma'aikatu da kmafanonin gwamnati, wadanda suka hada da Sakataren gwamnatin kasar, shugaban majalisar mutanen kasar, shugaban hukumar radiyo da Telebijin na kasar, shugaban kamfanin jiragen sama na kasar.
A halin yanzu an shiga mako na ukku kenan tun lokacinda mutanen kasar ta Sudan suka fara zanga-zangar neman shugaba Umar Hassan El-Bashir ya sauka daga mukaminsa.
A ranar 19 ga watan Decemban da ya gabata ne mutanen kasar sudan suka fara zanga zangar nuna rashin amincewa da tashin goron zabi na farashin kayakin abinci da bukatun yau da kullum a kasar.