Madagaska : Kotun Tsarin Mulki Ta Amince Da Zaben Rajoelina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34728-madagaska_kotun_tsarin_mulki_ta_amince_da_zaben_rajoelina
Kotun tsarin mulki a Madagaska, ta amince da nazara da dan takara Andry Rajoelina ya samu a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.
(last modified 2019-01-08T12:34:03+00:00 )
Jan 08, 2019 12:34 UTC
  • Madagaska : Kotun Tsarin Mulki Ta Amince Da Zaben Rajoelina

Kotun tsarin mulki a Madagaska, ta amince da nazara da dan takara Andry Rajoelina ya samu a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

Kotun ta kuma ayyana tsohon shugaban kasar Andry Rajoelina, mai shekaru 44 a matsayin zababen shugaban kasar, tare da yin watsi da dukkan korafen korafen da dan takaran da ya sha kaye Marc Ravalomanana ya gabatar mata, bayan zaben kasar zagaye na biyu na ranar 19 ga watan Disamba da ya gabata.

A ranar 19 ga watan Janairun nan ne ake sa ran rantsar dashi a matsayin shugaban kasar.

Mista Rajoelina ya dai lashe zaben ne da kashi 55,65% na yawan kuri'un da aka kada, a yayinda babban aboklin hammayarsa Marc Ravalomanana ya samu kashi 44,34%, sakamakon da dan takaran Ravalomanana ya yi watsi dashi yana mai zargin tafka magudi.

A kwana nan daruruwan magoya bayan dan takaran da ya sha kaye ne suka gudanar da zanga zanga ta nuna adawa da sakamakon zaben, tare da kira ga kotun tsarin mulkin da kada ta amince dashi.