An Rusa Wata Kungiyar Mai Alaka Da Da'esh A Kasar Moroko
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34734-an_rusa_wata_kungiyar_mai_alaka_da_da'esh_a_kasar_moroko
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Moroko ce ta sanar da rusa wata kungiya a arewacin kasar wacce take da alaka da kungiyar Da'esh
(last modified 2019-01-09T07:17:12+00:00 )
Jan 09, 2019 07:17 UTC
  • An Rusa Wata Kungiyar Mai Alaka Da Da'esh A Kasar Moroko

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Moroko ce ta sanar da rusa wata kungiya a arewacin kasar wacce take da alaka da kungiyar Da'esh

A jiya Talata ne ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Moroko ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa an rusa kungiyar ne a garuruwan al-Nador da Daryush da ke arewacin kasar

Bugu da kari majiyar ta ce an samu wasu na'urori na sadarwa da kuma makamai a tare da mutanen, haka nan littatafai na akidunsu

Sanawar ta kuma kunshi cewa mutane suna kan ganiyar shirya kai hare-haren ta'addanci ne a cikin kasar

A cikin watannin bayan nan kungiyar ta Da'esh ta kara kaimi wajen shirye-shiryen kai hare-hare a cikin kasar, sai dai jami'an tsaron suna samun nasara akansu

A cikin watan Disamba na 2018 ne 'yan ta'addar kasar ta Moroko su ka kashe masu yawon bude ido biyu tare da sare kawunansu