SHARHI : Bayyanin Hukumar INEC Kan Zaben Najeriya na 2019
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34748-sharhi_bayyanin_hukumar_inec_kan_zaben_najeriya_na_2019
A Najeriya a yayin da babban zaben na 2019 ke karatowa, hukumar zaben kasar mai zaman kanta cewa da INEC, ta sanar da cewa sama da 'yan kasar miliyan 84 ne suka ciri katin zabe a zaben kasar na watan gobe dake tafe.
(last modified 2019-01-10T05:13:46+00:00 )
Jan 10, 2019 05:13 UTC
  • SHARHI : Bayyanin Hukumar INEC Kan Zaben Najeriya na 2019

A Najeriya a yayin da babban zaben na 2019 ke karatowa, hukumar zaben kasar mai zaman kanta cewa da INEC, ta sanar da cewa sama da 'yan kasar miliyan 84 ne suka ciri katin zabe a zaben kasar na watan gobe dake tafe.

A bayyani da hukumar ta yi, ga shugabannin jam'iyyun siyasa a Abuja, shugaban hukumar ta INEC, Mahmood Yakubu, ya ce rajista na karshe na wadanda suka cancanci tsayawa don kada kuri'a a zaben na watan Fabariru mai zuwa ya kama mutum miliyan 84, 004,084.

Yawan wadanda suka cancanci yin zaben ya karu da kusan kashi 20%, idan aka kwantanta da waccen babban zaben kasar da ya gabata a shekara hudu da suka wuce, inda mutum sama da miliyan 68 suka ciri katin zabe.

A bayanin hukumar ta ce a arewa Maso yamma ne ya samu mafi yawan adadin wadanda suka yanki katin.

Yayin gabatar da jaddawalin karshe na wadanda suka yanki katin zaben, shugaban fannin katin zabe a hukumar, Iro Gambo, ya bayyana cewa mutum miliyan 20,158,100 ne suka yanki katin zabe a yakin Arewa maso yamma, wanda hakan ya basu damar zuwa na daya da kaso 24.06% daga cikin miliyan 84,004,084.

Ya kuma ce Kudu maso Yamma ce ta zo na biyu, da mutum miliyan 13,366,070, wato kaso 15.91%, sai Arewa ta tsakiya ta zo ta Uku, da miliyan 12,841,279 kaso 15.29% ke nan.

Arewa ta Gabas da Kudu maso Gabas ne suka zo na karshe ga adadin wadanda suka yanki katin da mutum miliyan 11,289,293 (13.44%) da miliyan 10,057,130 (11.91%).

Haka kuma bayyanin na INEC ya nuna cewa jinsin mata ne suka fi yankan katin zabe, inda aka samu mata miliyan 44,405,439 (52.86%), sai maza miliyan 39,598,645, wato kaso 47.14%.

INEC ta bayyana cewa, jihar Kano da Legas ne suka samu mafiya wadanda suka yanki katin zabe da mutum miliyan 6.6 (Kano) da kuma miliyan 5.5m (Legas).

Haka zalika a cewar hukumar ta INEC 'yan takara 73 da suka fito daga jam'iyyun siyasa 91 ne zasu fafata a zaben shugaban kasa. ciki harda shugaba mai barin gado Muhammadu Buhari, dake neman wani wa'adin mulki na biyu, inda zai fafata da babban abokin hammayarsa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. 

Za'a gudanar da zaben 'yan majalisa makwanni biyu bayan zaben shugaban kasa, inda 'yan a majalisar datijai, kujeru 109 ke zawarcin 'yan majalisa, sai kuma 360 daga bangaren majalisar dokoki, sai kuma zaben gwamnani a jihohi 29 daga cikin 36 a fadin kasar ciki harda Abuja babban birnin tarayya.

Hukumar ta INEC ta ce ta dauki kwararen matakai za zaben mai zuwa ciki harda yaki da saida kuri'a, kamar yadda aka gani a zaben jihar Ekiti, da amfani da wayar salula da kuma na'urar daukan hoto.

A ranar 16 ga watan Fabrairu mai zuwa ne al'ummar Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Nahiyar Afrika zasu kada kuri'a a babban zaben kasar.