ASUU Ta Ce Har Yanzu Ba Ta Janye Yakin Aiki Ba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34751-asuu_ta_ce_har_yanzu_ba_ta_janye_yakin_aiki_ba
Kungiyar Malaman jami'o'i a Najriya ta bayyana cewa ba ta ga wani abu a kasa ba, da zai sanya ta koma bakin aiki ba a tattaunawa da suke yi da gwamnatin tarayyar kasar.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Jan 10, 2019 12:20 UTC
  • ASUU Ta Ce Har Yanzu Ba Ta Janye  Yakin Aiki Ba

Kungiyar Malaman jami'o'i a Najriya ta bayyana cewa ba ta ga wani abu a kasa ba, da zai sanya ta koma bakin aiki ba a tattaunawa da suke yi da gwamnatin tarayyar kasar.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto majiyar Kungiyar tana cewa har yanzun bata ga wani abu a kasa a bangaren gwamnatin kasar wanda zai sa ta amince da dakatar da yajin aiki ba.

Kungiyar Malaman Jami'a a tarayyar Najeriya ASUU ta fara yajin aiki ne tun ranar 4 ga watan Nuwamban da ya gabata don tilastwa gwamnati ta amince da bukatunta na kashewa jami'o'in kasar Kudade, da kuma wasu hakkokin malaman na Jami'a.  

Wasu daga cikin wadannan bukatun dai, malaman jami'an sun cimma yerjejeniya da gwamnatocin da suka shude tun shekara 2013 ba tare da an cika su ba. 

A shekara ta 2013 gwamnatin tarayyar a lokacin ta amince ta kashe kudade naira Triliyon 1.3 kan gyare-gyare da kuma bukatun jami'o'in gwamnatin tarayyar Kasar, amma har yanzun bata cika wannan alkawarin ba.