An Kashe Masu Zanga -Zanga Ukku A Kasar Sudan
A ci gaba da tashe-tashen hankula a kasar Sudan a jiya Alhamis jami'an tsaron kasar sun kashe masu zanga-zanga biyu a garin Omdurman kusa da babban birnin kasar a lokacinda suka harbesu da bindiga. banda haka wasu mutane 8 suka ji rauni sanadiyar shakar hayaki mai sa hawaye.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa rikicin jiya Alhamis shi ne yafi muni tun lokacinda aka fara wannan tashin hankalin kimanin makonni ukku da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa tun lokacinda aka fara tashe-tashen hankulan sanadiyyar tashin farashin kayakin abinci musamman biredi a kasar, ya zuwa yanzu an kashe mutane fiye da 40.
Masu zanga-zanga dai suna bukatar saukar shugaban kasar ta sudan Umar Hassan albashir daga mukaminsa, bayan ya gaza kyautata rayuwar mutane.
A ranar 19 ga watan Decemban da ta gabata ce aka fara zanga- zangar ganin bayan shugaban, wanda ya share fiye da shekaru 25 yana shugabancin kasar.