DR Congo : Fayulu, Ya Bukaci A Soke Sakamakon Zabe
Dan takaran adawa da ya zo na biyu a zaben shugaban kasa na Jamhuriya Demokuraddiyar Congo ya gabatarwa da kotun tsarin mulkin kasar korafinsa akan zaben da aka gudanar a ranar 30 ga watan Disamba da ya gabata.
A cikin takardar da ya gabatar mai dauke da korafinsa, dan takara Martin Fayulu, ya bukaci kotun data soke sakamakon da hukumar zaben kasar ta sanar na zaben shugaban kasa, wanda ya ayana dan takaran adawa gudan, Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben.
M. Fayulu wanda ya kuma zargi hukumar zaben kasar da murda sakamakon zaben domin ayyana M. Tshisekedi a matsayin shugaban kasa, ta hanyar hadin kan shugaba mai barin gado Joseph Kabila, ya kuma bukaci da a sake kidayar kuri'un da hannu.
A yanzu kotun tsarin mulkin kasar na da nan da kwanaki takwas domin duba korafen korafen da dan adawan ya gabatar mata.
A sakamakon da hukumar zaben ta CENI, ta fitar dan takara Félix Tshisekedi ne ya lashe zaben da sama da kashi 38%, a yayin da dan takaran adawan guda, Martin Fayulu, ke biye masa da kashi 34%, sai kuma dan takara jam'iyya mai mulki, Emmanuel Ramazani Shadary, da ya zo na uku da 23% na yawan kuri'un da aka kada.
Tuni dai wasu kasashen yamma da suka hada da Belgium wacce ta yi wa kasar ta DR Congo mulkin mallaka da kuma Faransa suka bayyana shakkunsu akan sahihancin sakamakon zaben da hukamar ta CENI ta fitar.