Shugaban Kotun Kolin Najeriya Zai Bayyana A Gaban Kotun Abuja
Shugaban kotun kolin Najeriya, mai matsayin alkalin alkalan kasar, zai gurfana gaban kotu kan zarginsa da rashin bayyana dukkan kaddarorinsa kamar yadda dokar kasar ta tanada ga duk wani mahaluki mai rike da babban mukami a kasar.
Kakakin kotun da'a ma'aikata na kasar, Ibraheem Al-Hassan, ya ce a gobe Litini ne alkalin alkalan kasar, Walter Samuel Nkanu Onnoghen, zai gurfana gaban wata kotun Abuja.
Kakakin kotun da'ar ma'aikatan bai fayyace takamaimai zargin da ake wa alkalin alkalan ba, saidai wasu majiyoyi daga gwamnatin kasar sun ce ana zarginsa da mallakar asusun ajiyar kudade na kudaden dalar Amurka, da kudaden turai (Euro) da kuma na Biritaniya.
A Najeriya dai dokar kasar ta tanadi duk wani babban jami'in gwamnati ya bayyana kaddarorin da ya mallaka, sannan basu da hurimin mallakar asusun kudade na kasashen ketare.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake zargin wani babban jami'an Najeriya da yin karya wajen bayyana kaddarorinsu, inda ko a cikin shekara 2015, aka zargi shugaban majalisar dattijan kasar, Bukola Saraki, da yin karya wajen bayyana kaddarorinsa a lokacin da yake rike da mukamin gwamnajin jihar Kwara a tsakanin shekara (2003-2011).
Saidai daga baya kotu ta wanke shi daga wannan zargin a watan Yuni na shekara 2016, matakin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, ta nuna rashin gamsuwa dashi.