An Tsawaita Wa'adin 'Yan Majalisar Dokoki A Guinea
Shugaba Alpha Conde, na Guinea, ya bada umurnin tsawaita wa'adin 'yan majalisar dokokin kasar.
A cikin daren jiya 12 ga watan Janairu nan ne wa'adin shekaru biyar na 'yan majalisar dokokin kasar ya kawo karshe.
Kudirin shugaban kasar dai ya kawo karshen ayar tambayar da aka dade ana azawa kan makomar 'yan majalisar dokokin kasar a daidai lokacin da wa'adinsu ya cika.
Kamar yadda ayar doka mai lamba 60, ta kundin tsarin mulkin kasar ta tanada, 'yan majalisar na da wa'adin aiki na shekaru shekaru biyar, saidai majalisar na da hurimin ta ci gaba da aiki, mudin ba'a gudanar da zaben 'yan majalisar ba.
Kafin dai ya sanya hannu kan kudirin, saidai shugaban kasra ya nemi izinin kotun tsarin mulkin kasar wacce ta bashi damar yin hakan.
Ana alakanta matakin tsawaita aikin 'yan majalisar da shirye shiryen da ake na girka hukumar zaben kasar da kuma gyaran fuska wa kundin zaben kasar.