Kungiyoyin Sun Sake Kiran A Fito Zanga zanga A Sudan
(last modified Sun, 13 Jan 2019 10:34:21 GMT )
Jan 13, 2019 10:34 UTC
  • Kungiyoyin Sun Sake Kiran A Fito Zanga zanga A Sudan

A Sudan, wasu kungiyoyin kwadaga sunyi kira da a sake fitowa zanga-zanga kin jinin gwamnati a manyan biranen kasar ciki harda Khartoum babban birnin kasar.

Kungiyoyin da suka yi kiran zanga zangar sun hada dana likitoci, malamman manyan makarantu da kuma injiniyoyi. 

Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka doshi wata guda ana zanga zanga mai nasaba da tsadar rayuwa a kasar ta Sudan.

Kafin boren ya koma na kyammar gwamnati, an soma zanga zanga ne kan matakin gwamnatin na kara farashin bredi da iskar gas.

Alkalumman da mahukuntan kasar suka fitar a baya bayan nan sun nuna cewa mutum 24 ne suka mutu tun bayan zanga zanagr data barke a ranar 19 ga watan Disamba na shekara data shude.

Shugaba Omar Hassan El-Bashir, na shugabancin kasar ta Sudan ne tun bayan juyin mulkin shekara 1989.