Hare-hare Na Barazana Ga Ci-gaban Yammacin Afrika Da Yankin Sahel
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34788-hare_hare_na_barazana_ga_ci_gaban_yammacin_afrika_da_yankin_sahel
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yawan hare-hare na barazana ga ci gaban yammacin Afrika da yankin Sahel.
(last modified 2019-01-13T10:38:13+00:00 )
Jan 13, 2019 10:38 UTC
  • Hare-hare Na Barazana Ga Ci-gaban Yammacin Afrika Da Yankin Sahel

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yawan hare-hare na barazana ga ci gaban yammacin Afrika da yankin Sahel.

Da yake bayyana hakan wakilin MDD mai kula da shiyyar ga kwamitin sulhun MDD , ya ce karuwar hare haren kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin addini, wadanda suke yin amfani da karin dabaru irin na zamani, hakan na haifar da koma baya ga cigaban kasashen yammacin Afrika da yankin Sahel.

"Duk da matakan soji, da ake dauka, amma hakan bai wadatar ba" inji Mohamed Ibn Chambas, inda kuma ya jaddada bukatar daukar matakan da suka dace.

A yankin tafkin Chadi, akwai karuwar hare haren mayakan Boko Haram a watannin baya bayan nan, sannan ana cigaba da samun rikicin manoma da makiyaya, duk da cewarsa rikicin na manoma da makiyaya ya dan ragu. 

A Nijar, har yanzu, ana fuskantar kalubaloli a yankunan yamma da kudancin kasar,

Wakilin MDDr yace, akwai bukatar daukar matakan da suka dace, kasancewar a cikin watanni 6 masu zuwa shiyyar zata tunkari manyan zabuka masu yawa da suka da kasashen Najeriya, Senegal, Mauritania da jamhuriyar Benin.