Kungiyar (SADC), Ta Bukaci A Sake Kidayar Kuri'un Zabe A D.R Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34793-kungiyar_(sadc)_ta_bukaci_a_sake_kidayar_kuri'un_zabe_a_d.r_congo
Kungiyar ci-gaban kasashen kudancin Afirka (SADC), ta bada shawarar a sake kidayar kuri'un zabe a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, domin kwantar da hankali a takaddamar data kunno kai bayan sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar.
(last modified 2019-01-14T06:37:47+00:00 )
Jan 14, 2019 03:34 UTC
  • Kungiyar (SADC), Ta Bukaci A Sake Kidayar Kuri'un Zabe A D.R Congo

Kungiyar ci-gaban kasashen kudancin Afirka (SADC), ta bada shawarar a sake kidayar kuri'un zabe a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, domin kwantar da hankali a takaddamar data kunno kai bayan sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a jiya Lahadi, ta kuma bukaci hukumomin kasar ta Congo dasu kafa gwamnatin hadin kan kasa wacce zata hada dukkan bangarorin siyasa na kasar.

Da yake sanar da hakan shugaban karba-karba na kungiyar ta SADC, kana shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, ya ce irin wannan yarjejeniyar zata taimaka ainun wajen shawo kan kiki-kakar da biyo bayan sanar da sakamakon wucin gadi na shugaban kasar, tare kuma da kira ga 'yan siyasar kasar dasu kai zuciya nesa.

Rahotanni sun nuna cewa tuni kawacen dake goyan bayan dan takaran da ya zo na biyu a zaben Martin Fayulu, ya amince da bukatar da kungiyar ta SADC ta gabatar na kafa gwamnatin hadin kan kasa, amma da sharadin a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

A cikin daren ranar Laraba data gabata ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta DR. Congo, ta sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar da aka kada kuri'arsa a ranar 30 ga watan Disamban na shekara data shude.

Sakamakon dai ya nuna dan takara adawa Felix Tshisekedi, ne ya yi nasara a zaben da sama da kashi 38% na yawan kuri'un da aka kada, a yayinda gudan dan adawan Martin Fayulu ke biye masa da sama da kashi 34%, sai kuma dan takaran jam'iyya mai mulki dake samun goyan bayan shugaban kasar mai barin gado oseph Kabila, cewa da Emmanuel Shadary Ramazani ya zo na uku.

Saidai jim kadan da sanar da sakamakon dan takaran adawa da ya zo na biyu a zaben, M. Fayulu ya yi fatali da sakamakon wanda ya ce yana cike da magudi inda kuma tuni ya mika korafe korafensa ga kotun tsarin mulkin kasar, wacce ita kuma take da kwanaki takwas bayan gabatar da korafin na ta amince dasu ko tayi watsi dasu.

Dama dai kafin hakan wasu kasashen turai da suka hada da Faransa da Belgium wacce ta yi wa kasar ta DR Congo mulkin mallaka suka bayyana shakkunsu akan sahihancin sakamakon zaben wucin gadin da hukamar ta CENI ta fitar.