Sudan : Jami'an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Bore A Khartum Da Darfur
(last modified Mon, 14 Jan 2019 04:14:37 GMT )
Jan 14, 2019 04:14 UTC
  • Sudan : Jami'an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Bore A Khartum Da Darfur

Jami'an kwantar da tarzoma a Sudan, sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zangar kin jinin gwamnati a Khartoum babban birnin kasar da kuma yankin Darfour.

Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne karon farko da zanga zangar da ake kan tsadar rayuwa wacce daga bisani ta rikide zuwa ta kyammar gwamnatin Umar El-Bashir ta bazu zuwa yankin Darfour dake yammacin kasar.

Masu zanga zangar a jiya Lahadi wadanda mafi yawa mata ne, na raira taken neman ''zaman lafiya, adalci da kuma yanci'', asalin salon da aka fara zanga zanga dashi a ranar 19 ga watan Disamba da ya gabata.

A jiya ne dai wasu kungiyoyin da suka hada dana likitoci, malamman manyan makarantun boko da kuma injiniyoyi a kasar ta Sudan sukayi kiran a fito wata sabuwar zanga zanga domin matsin lamba wa gwamnatin kasar.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka doshi wata guda ana zanga zangar mai nasaba da tsadar rayuwa a kasar ta Sudan.

Kafin boren ya koma na kyammar gwamnati, an soma zanga zangar ne kan matakin gwamnatin na kara farashin bredi da iskar gas.

Alkalumman da mahukuntan kasar suka fitar a baya bayan nan sun nuna cewa mutum 24 ne suka mutu tun bayan soma zanga zanagr data barke a wasu sassan kasar a tsakiyar watan da ya gabata.

Shugaba Umar Hassan El-Bashir, na shugabancin wannan kasa ta Sudan tun bayan juyin mulkin da ya yi a cikin shekara 1989.