An Tsawaita Dokar Ta Baci Da Watanni Uku A Masar
(last modified Mon, 14 Jan 2019 05:50:09 GMT )
Jan 14, 2019 05:50 UTC
  • An Tsawaita Dokar Ta Baci Da Watanni Uku A Masar

Majalissar dokokin kasar Masar, ta amince da kara wa'adin dokar ta baci a wasu yankunan kasar da watanni uku.

Matakin dai ya biyo bayan matsalolin tsaro da aka fuskanta a lardunan kasar na Gharbiya da Alexandria.

Kamfanin dallancin labarai na MENA ya bayyana cewa, majalissar ta amince da kudurin doka da shugaban kasar ta Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya gabatar, na neman tsawaita wa'adin dokar da watanni uku, wanda kuma za ta fara aiki tun daga ranar 15 ga watan nan na Janairu.

Karkashin tanajin dokar, sojoji da 'yan sanda za su iya daukar dukkan wani mataki na yaki da 'yan ta'adda, tare da tabbatar da tsaro a daukacin sassan kasar.

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi ya kaddamar da dokar ta bacin a karon farko ne a watan Afrilun shekarar 2017, biyowa bayan tagwayen hare haren bama bamai da aka kai a lardunan na Gharbiya da Alexandria dake arewacin kasar, lamarin da ya hasaran rayukan mutane a kalla 47, tare da raunata wasu sama da 100.