Gabon : Ali Bongo Ya Koma Libreville
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34815-gabon_ali_bongo_ya_koma_libreville
Shugaba Ali Bongo Odimba na Gabon, ya koma kasarsa a cikin daren jiya Litini, bayan shafe sama da wata biyu na jinya a kasashen waje.
(last modified 2019-01-15T16:15:47+00:00 )
Jan 15, 2019 16:15 UTC
  • Gabon : Ali Bongo Ya Koma Libreville

Shugaba Ali Bongo Odimba na Gabon, ya koma kasarsa a cikin daren jiya Litini, bayan shafe sama da wata biyu na jinya a kasashen waje.

Kamar yadda kafofin yada labarai da dama daga kasar suka rawaito, sun ce jirgin shugaban kasar ya sauka a Libreville a cikin daren jiya wajewar wanann safiyar Talata.  

Bayanai sun nuna cewa shugaba Bongo, zai halarci bikin rantsar da sabuwar gwamnatin kasar, wanda zai kasance bayyanarsa ta farko bainar jama'a tun bayan jinyar da fara da farko a Saudiyya a ranar 24 ga watan Oktoba na shekara 2018 data shude.

Saidai a cewar jaridar ''La tribune'' a kasar shugaban zai koma kasar Morocco domin ci gaba da jinya.

Komawar da Mista Bongo ya yi a kasarsa na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan murkushe wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar.

Jinyar da shugaban kasar ta Gabon, Ali Bongo ya fara a watanni biyu da dai haddasa kace-nace ba kadan ba a kasar ta Gabon.