An Kashe Tare Jikkata Mutane 17 A Harin Ta'addanci A Kasar Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34822-an_kashe_tare_jikkata_mutane_17_a_harin_ta'addanci_a_kasar_kenya
Majiyar tsaro daga kasar Kenya ta ce ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 3 yayin da wasu 14 su ka jikkata
(last modified 2019-01-16T03:48:03+00:00 )
Jan 16, 2019 03:48 UTC
  • An Kashe Tare Jikkata Mutane 17 A Harin Ta'addanci A Kasar Kenya

Majiyar tsaro daga kasar Kenya ta ce ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 3 yayin da wasu 14 su ka jikkata

A jiya Talata da rana ne, aka ji fashewar wasu abubuwa da kuma harbe-harbe a tsakiyar birnin Nairobi na kasar Kenya.

Baban jami'in 'yan Sandan kasar ta Kenya Philip Ndolo ya bayyana cewa; An rufe yankin da aka kai harin da hana shiga da fita

Shedun ganin ido sun ce; sun ga harshen wuta yana tashi a wurin da aka kai harin, da kuma wasu motoci da suke cin wuta

Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabab da ke kasar Somaliya ta sanar da cewa ita ce ta kai harin

Wannan dai ba shi ne harin farko da kungiyar ta al-shabab ta kai a kasar ta Kenya ba. A cikin watan April na 2015 kungiyar ta kai hari a jami'ar "Garisa" wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 148

A cikin 2011 ne kasar Kenya ta aike da sojojinta zuwa kasar Somaliya domin yakar kungiyar al-shabab mai alaka da alka'ida